• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Friday, March 31, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Dan Takarar Gwamna A Jam’iyyar SDP Ya Yi Wa Masu Zagayen Maulidi Sha-tara Ta Arziki A Katsina.

October 30, 2022
in Sashen Hausa
0
Dan Takarar Gwamna A Jam’iyyar SDP Ya Yi Wa Masu Zagayen Maulidi Sha-tara Ta Arziki A Katsina.
0
SHARES
62
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Mohammad A. Isa, Katsina.

Dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar SDP mai alamar Doki, Alhaji Ibrahim Zakari Talba ya raba kayan arziki a yayin zagayen Maulidin zagayen gari duka da aka gabatar a ranar Lahadin nan.

Kamar yadda wakilinmu ya labarto mana a lokacin da yake zantawa da masu jagorantar rabon kayayyakin, wani Jamilu da Aliyu Basa, sun bayyana masa cewa; rabon kayan da dan takarar ya yi wa al’umma wanda Muhammad Tukur Makama Bakori ya dauki nauyin aiwatarwa a mamadinsa, an yi ne saboda nuna so da kauna ga fiyayyen Allah Annabi Muhammadu(S)

Har wayau, masu rabon sun kuma bayyana cewa, sun rarraba kayayyakin ne a yankuna Uku na Birnin a wannan rana ta zagayen Maulidin Gari Duka, don dai farantawa al’ummar Annabi kamar yadda dan takarar gwamnan Alhaji Ibrahim Zakari Talba yake da burin yi a ko da yaushe.

Bugu da kari, Aliyu Basa ya kuma bayyana cewa, an buga Katon din ruwa da Lemu kimanin dubu goma (10,000) inda tuni kuma suka jagoranci raba su ga daukacin al’umma masoya Manzon Allah(S) wadanda suka fito kallo da kuma masu zagayen Maulidi a wannan rana.

Su ma jama’a wadanda suka amfana da rabon kayayyakin sanyaya Makogwaron, sun bayyana jin dadinsu matuka bisa ga yadda wannan dan takarar gwamna ya kawo masu wannan gudummuwa a lokacin da makogwaransu ya ke bukatar hakan, inda ya jika masu shi da wadannan kayyakin alheri musamman ma duba da yadda kayayyakin suka zo masu a daidai lokacin da suka fi bukatarsu, wato sa’ilin da makogwaro ke bukatar a sanyaya shi.

Ranar “Zagayen Maulidin Gari Duka” (kamar yadda al’umma ke kiransa), rana ce muhimmiya ga al’ummar garin Katsina masu yin Maulidi, inda jama’a ke fitowa kwansu da kwalkwatarsu wajen kallon zagayen Maulidin Annabi(S), ranar da take a matsayin ranar karshe ta zagayen Maulidi a watan Rabi’ul-Awwal, zagaye “Bugun Tashi” wanda daga shi ba wani sai kuma na wata shekara in Allah ya kai mu.

Share

Related

Source: Katsina City News
Via: Zaharadeen
Previous Post

MASU GARKUWA DA MUTANE A GARIN DANDUME

Next Post

THE KADUNA REFINERY IS NOW SET FOR COMPLETE REHABILITATION! PositiveFactsNG

Next Post
THE KADUNA REFINERY IS NOW SET FOR COMPLETE REHABILITATION!  PositiveFactsNG

THE KADUNA REFINERY IS NOW SET FOR COMPLETE REHABILITATION! PositiveFactsNG

Recent Posts

  • On birthday, clerics pray for Tinubu, Nigeria in Abuja
  • Gwamna Masari ya Kaddamar da Kwamitin Miƙa Mulki ga sabuwar Gwamnati
  • Masari: Tinubu Na Bukatar Addu’a
  • Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Karu Zuwa N46.25tr —DMO
  • FEC Approves N59.78bn For Ogoni Cleanup Projects

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In