…Don ramuwar gayya
…..Don wasu dabbobi
Misbahu Ahmad Batsari
@ katsina city news
Da yammacin ranar talata 06-12-2022 wasu gungun ƴan bindiga dake kan babura sama ga ɗari sukayi ma ƙauyen Daurawa da Garin-Ajiya dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina ƙawanya.
Ƴan bindiga sun dira ma ƙauyukan cikin shirin yaƙi suna harbi ta kowa ne lungu da saƙo, suyi ta ƙona rumbuna da shaguna tamkar ba zasu bar komai ba a garin.
Haka kuma wasu shaguna sun sace kayayyakin masarufi tare da ƙona rogowar bayan sun kwashe waɗanda ransu yayi masu ɗaɗi. sun shafe kimanin awonni ukku suna cin karen su ba babbaka.
Sun kashe mutune shidda wasu kuma suna asibiti ana yi masu magani.
wani da yasha daƙyar ya bayyana mana cewa jami an tsaro sun kai masu ɗauki.
Wani bincike ya nuna cewa ana zaton dabar Ɗan ƙarami ce ta kai wannan hari, saboda wani da ya nemi a sakaya sunansa ya labarta mana cewa sunji ƙishin-ƙishin cewa Gwaska Ɗan ƙarami yace zaije yankin gaisuwa da roƙon iri domin a cikin makon da ya gabata jirgi yakai hari har ya rutsa da gidan Ɗanɗa wanda ɗan uwa ne gare shi kuma yayi masa ɓarna sosai, sannan dama shi Ɗanɗa yana zaune ne a yankin na Daurawa. wata majiya kuma tace harin bai rasa nasaba da wani garken tumaki da jami’an tsaro suka kama a yankin saboda ɓarna da suke yi na kayan amfanin gona. Wanda hakan yasa ɓarayin daji suka shigo garin kwanaki ukku kafin wannan harin inda nan take suka buɗe wuta suka kashe mutum biyu, wani kuma mutum ɗaya yasha da harbin bindiga.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245