Wata takarda mai ɗauke da sanya hannun Gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban yaƙin neman Zaɓen Tinubu/Shatima a Arewa maso Yamma, Dakta Bello Matawallen Muradun, ta tabbatar da Alhaji Masa’udu Abdulƙadir (Dan Guruf) a matsayin jami’in Tuntuɓa, shawara da wayar da kan jama’a na yaƙin neman Zaɓen Tinubu a Arewa maso yammacin Najeriya.
Alhaji Masa’udu Abdulƙadir Dan Guruf, Ɗan Asalin jihar Katsina, ɗan Kasuwa da ya kasance a jam’iyyar PDP a baya wanda a yanzu ya bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai Mulki, ya samu wannan Babban muƙami ne duba da yanda yake zaƙaƙuri kuma jajirtacce Wajen Siyasa da wayar da kan jama’a don su fahimci ina Siyasa tasa a gaba. Wanda aka bayyana shigarsa jam’iyyar APC zuwa yanzu ya zabaro manya kuma jiga-jigai a jihar sa da wasu jihohi, gami da Matasa da dama suka bar jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar APC.
