
A kokarin ganin APC ta samu Nasara a Dukkanin Zabuka masu zuwa, kungiyar da ke marawa Zaɓaɓɓen Ɗantakarar Shugaban ƙasa Bola Ahamed Tinubu da Dikko Radda baya ta shiga ƙananan hukumomi bakwai don rakiya ga Ɗantakarar Gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Umar Raɗɗa a wajen yakin neman zabensa.
Zagayen yakin neman zaben da aka fara kaddamar da shi a karamar hukumar Faskari, tare da Dandazon ‘Yan Kungiyar daga nan sai aka juya zuwa shiyyar Daura, aka shiga karamar hukumar Baure, Zango, Sandamu, Mai adua, Daura, a ranar Litinin kuma akazo garin Mashi duk a yankin Daura. Dondazon magoya bayan jam’iyyar APC ne ke tarbar ‘Yantakar, wanda Jagora kuma Shugaban kungiyar na Dan Guruf Support for Tinubu 2023 ya yaba ga yanda Jam’iyyar su ke samun karɓuwa a ko ina.
Ana saran Kungiyar ta Dan Guruf Support for Tinubu 2023 zata taka duka fadin jihar Katsina saboda tace Dikko da Tinubu nata ne. Alhaji Masa’udu Abdulƙadir Dan Guruf shine shugab mai bd shawara da wayar da kan jama’a a kwamitin yakin neman zaben Dantakarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a Arewa maso yamma