Kamar yanda suka bayyana a wajen taron Kaddamar da fara yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shatima Dikko/Jobe a karamar hukumar Faskari. Kungiyar da masoya na haƙiƙa masu marawa Alhaji Mas’udu Danguruf baya a Siyasar sa, ƙarƙashin jagorancin Alh. Ghali Yusuf, sunce basu da haufi ko shakka cewa APC zata samu dubun kuru’u ta hanyar masoyinsu Alh. Dan Guruf.

Taron da akayi a garin Faskari wanda “Dan Guruf Support for Tinubu 2023 suka ja tawagar masoya APC daga garin Katsina zuwa Faskari ya kayatar inda inda Magoya bayan APC a ƙarƙashin jagorancin Dan Guruf, sukaita ɗaɗɗaga Tutoci da Banoni, na nuna goyon bayansu ga APC da jagoran Tafiyar su, Alhaji Masua’udu Abdulkadir.