Nasir Lawal Kurfi
Gidauniyar United Nation Industrial Development Organization (UNIDO) karkashin Majalissar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar Opportunities Hub ta zabi Comrade Nasir Lawal Kurfi dan’asalin jihar Katsina a cikin jerin jajirtattun Matasa É—ari (100) na duniya da babban Mawakin Hip-hop wanda akafi sani da Davido domin jajircewasu wajen hidima ga jiharsu ga Jama’a da Kuma kasa baki daya.
Wannan zaben ya biyo bayan tantance wa da cmKwamitin kwararru na duniya suka yi masu tare na tsawon wata shida.
Daga karshen Comrade Nasir Lawal ya Miƙa godiyarsa wajen mai girma Gwamnan Jikar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, CFR domin irin tallafi da Kuma gudummuwar da yake bawa Matasan Jihar Katsina.