Malam Ibrahim Muhammad Gamawa na daga cikin Marubutan harkar Musulunci da Sheikh Zakzaky ke jagoranta kuma shugaban Cibiyar Imam Mahadi Foundation Cibiyar da ke Gwagwarmaya don Tabbatar da Adalci a ko wane Mataki, dake da Hedikwata a Abuja, ya samu zuwa Katsina a wajen Bikin Zagayen Maulidi tare da Sheikh Abdulrahama Yola inda aka gansu cikin Sahun zagayen Maulidi. Dandalin Media Forum Katsina ya samu zantawa da su ga kadan daga cikin Firar:
Malam Ibrahim Gamawa: “Aƙwai wani ɗan’uwa bawan Allah Jajirtacce wanda muke Gwagwarmaya dashi a Abuja Kwatsam sai aka cemana Mahaifiyarsa ta Rasu! danaji wannan Mutuwar na jima cikin dan lokacinnan banji mutuwa irin wannan wadda ta ɗimautani ba shi ne yasa muka taso daga gidajenmu domin yin wannan ta’aziyyar, a garin Ɗanja dake jihar Katsina”.
Gamawa yace: “Mun Shaku da Ita Mahaifiyar tasa, saboda a kwanakin baya Lokacin wata Muzaharar neman ‘Yancin Jagora, da muka zo mun biya wajenta taimana Shatara ta Arziki, daukemu matsayin ‘Ya’yanta har Bidiyo da Hotunan ziyarar mu wajenta na dauka. To kasan sabanin yanayin da Ƙasa take ciki kada ka dorawa Mutum ɗawainiya shi ne mukace bari muzo Katsina mukwana washe gari mu wuce sai mukaji za’ayi zagayen Maulud sai mukace bari mutsaya mushiga sahu ayi damu washe gari sai mu wukuce, tunda bazaiyiyu mukoma Zariya cikin wannan dare ba!, sana har wayau akan hanyar Zariya Inada wasu ‘yan Ziyarce-ziyarce.” Yace wannan shine dalilin zuwanmu garin Katsina dani da Abokin tafiya ta Malam Abdulrahama Yola.
A cikin Tattaunawar da Malam Gamawa a Masaukinsa tare da wakilan Media Forum Katsina. A kwai cikakkiyar tattaunawar ta Bidiyo da zamu kawo maku a kafafen Katsina Media Forum mai tsawon mintina Talatin. Ku kasance da kafafen Sadarwa na Katsina Media Forum.