Rundunar ƴan sanda a jihar Kano, ta kama wani matashi mai suna Gaddafi Sagir, bisa zargin kashe kishiyar mahaifiyarsa, da ƴar ta mai shekara takwas.
A wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar a Fadama Rijiyar Zaki da ke Karamar Hukumar Ungogo bayan da mahaifin matashin ya dawo ya sami matarsa, Rabi Sagir, da ƴar ta ta, wacce yar riƙo ce, Munawwara, kwance jina-jina.
Sanarwar ta ƙara da cewa bayan da rundunar ‘yan sandan jihar ta samu labarin abin da ya faru, nan take ta aika jami’anta zuwa wajen, inda bayan an kai matar da kuma yarinyar Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad ne likita ya tabbatar da rasuwarsu.
An dai kama wanda ake zargin ne a wani kango a kokari da yake na tserewa ya bar jihar.
A binciken farko da aka gudanar, wanda ake zargin ya amsa laifinsa na yin kisan inda ya ce ya yi amfani da sukun-direba wajen daɓawa kishiyar babar ta sa a wuya da kuma kai sannan ta shake ‘yarta da ɗankwali har sai da ta daina numfashi.
Da ake tambayar sa dalilin aikata kisan, Gaddafi ya ce ya yi hakan ne sabo da marigayiyar ta takura wa mahaifiyarsa.
“Har ta kai ga mahaifiya ta ta bar gidan ta koma garin mu. Ta kuma hada mahaifi na da mahaifiya ta, ta sanya ya na yi mata wulakanci iri-iri. Ni kuma hakan na ɓata min rai,” in ji matashin.
A cewar sa, rigima ce ta kare tsakanin sa da marigayiya Rabi da safe, lokacin da ya zo ɗaukar abinci, inda ya ƙara da cewa shi ne ya ɗauki sukindireba ya buga mata a wuya.
Ya ƙara da cewa ita ma Munawwara ɗin ya shake ta ne da kyalle zani sabo da ta “buga mun taɓarya a ka. Shi ne ita ma ma shake ta.”
Ya ce shi ba ya shaye-shaye kawai dai sharrin zuciya ne ya sanya ya aikata wannan ta’asar.
Sai dai kuma ya nemi a yi masa afuwa.