Daliban kwalejin ilimi ta Cognet da ke cikin karamar hukumar jahar Katsina, tsangayar LafiyarAl’umma wato (Public Health) sun gabatar da ilimintar da Al’umma tare da basu tallafi a kauyen Bakuru da sabon Gida wannan yafarune saboda Ilimin da makarantar ke koyar dasu da ya shafi kare Al’umma daga cututtuka da fadakar da al’umma akan kula da lafiyar jikinsu da muhallansu, wannan fadakarwa da sukayi tare da Tallafawa al’umma na matsayin wani sashen jarabawa na abinda suke karanta, a wani darasi da ake cewa Ilimin isar da sako da sadarwa wato (information Education and communication)
Yayin wannan fadakarwa ga al’umma da daliban suka aiwatar sun gabatar da fadakarwar kan tsabtace muhalli da kuma masassarar ciwon sauro inda suka fadakar kan abubuwan da ke haddasawa da kuma mataki idan ankamu tare da daukar matakan kariya, daliban su samu rakiyar wasu daga malamai na cikin makaranta da na waje.
Daliban kwalejin lafiyar, bayan sun fadakar sun rararraba kayan tallafi da suka hada da maskito, omo na wanki. Domin magance sauro da kuma tsabtace muhalli.
A duk inda suka halarta sun samu tarbar mai Unguwa ko maigari sannnan Al’ummar yankin sunnuna farinciki tare da yi musu fatan Alkhairi.