Malam Sabo musa mai taimakawa Gwamnan Katsina na musamman akan maido da al’amura Daidai da muhallansu, yayi wannan jawabin ne a wajen bikin rantsar da ‘Ya’yan kungiyar MOPPAN ta kasa reshen jihar Katsina.
Malam Sabo musa yace “Yanzu ba lokacin yin siyasa da matsalar tsaro bane, wannan matsala ce da take bukatar hada kai da duk wani mutum ko daga wace jam’iyya ya fito domin tunkarar kawo karshen wannan matsala.”

Ya kara da cewa; a da idan zaka kano ko Abuja shekarun baya sai kayi awa biyar ko goma sha, saboda Checking Point, sakamakon irin yanda Boko Haram suka shiga cikin garin Kano suka tada Bom, suka shiga cikin garin Abuja suka tada Bom a Hedkwatar’Yansandan Najeriya, amma yanzu abin yazama Tarihi injishi.
Yace muyi addu’a dama Allah yace zai jarabemu da abubuwa, iri-iri na daga tsoro, da yunwa, da talauci, da zubda jini. Yace idan wadannan matsaloli suka faru, sai Allah yace kuce Innalillahi wa’inna ilaihiraji’una. Saboda haka maganar hada tsaro da siyasa a bari. S.A Sabo Musa yace yanzu Allah ya kawo mu wani jarabi na Masu garkuwa da mutane, wanda yake bukatar hadin kai ga dukkanin mu domin magance matsalar.
Sabo Musa yace: game da harkar tsaro a nan jihar Katsina kowa yasan abinda ake, ga Sojoji da ‘Yansanda nan, ku kungiyar MOPPAN, Tunda kungiya ce ta wayar da kai, kungiya ce ta ‘Yan Film to yakamata ku karantar da Al’umma cewa, sojojin nan da ‘yansandan nan ba na Gwamnatin jiha bane, na Gwamnatin tarayya ne, suna amsar Umarni daga sama. Yanzu idan mai girma Gwamnan jihar Katsina zaice ga abinda yake so, to sai sun nemi umarni daga sama, yace da na jihar Katsina ne, da nan take zai bada umarni, kai bama Gwamna ba ko Sakataren Gwamnati zai iya bada Umarni, kuma a aikata abinda yadace.
Sabo musa ya ce duk bukatun da ake so game da maganar tsaro gwamnatin jihar Katsina tana badawa, yace don haka lallai ne gareku ku karantar da mutane wannan matsalar, afidda maganar Siyasa, saboda idan barayin nan sunzo dauka, suna daukar dan PDP, suna daukar dan APC daga ko wace jam’iyya kake sai sun dauke ka. Yace su barayinnan babu ruwansu da siyasa, don mi mu kuma zamu dunga dangana abin da siyasa. Malam Sabo Musa yace, idan wannan matsalar tazo babu wanda take ragawa, andauki mai kudi andau Basarake Andau mai mulki andau, talaka, hatta mai fura da Nono, dauka suke.
A karshe yayi kira da babbar mura ga kungiyar cewa su faɗakar musamman matsalolin da mafiya yawa Infomas ne ke haddasa su, don haka kungiyar ta faɗakar akan wannan matsala, ba zance ba ne na soyayya, ko wani abu, yanzu lokaci ne na neman zaman lafiya, a faɗakar da mutane, inyaso idan an samu zaman lafiya komi za’ayi sai aje ayi. Sabo musa ya bada misalai akan irinsu Kasumu yaro, da marigayi Danjuma Katsina da Fina-finan su da litattafan su, yace sunyi rubutun ne a daidai da zamanunsu da irin matsalolin da suke faruwa a wancen zamanin, yace to ashe kunga haka akeyi, domin magance matsalolin da suka addabi zamanin.
Angudanar da bikin rantsuwa a dakin taro na tsohin gidan Gwamnatin jihar Katsina a ranar Lahadi 4 ga watan Satumba 2022.