Da alama babban bankin Najeriya CBN ya fara cika alkawarin da ya daukar wa ‘yan kasar na fara fitar da tsaffin takardun Naira.
Kawo yanzu dai bayanai daga babban birnin tarayyar kasar Abuja na cewa ‘yan Najeriya sun fara samun kudade a ciki da wajen bankuna cikin sauki, ba kamar watannin da suka gabata da neman takardun kudi ke zama babban tashin hankali ba.
Wannan ci gaba dai na zuwa ne bayan da kungiyar kwadago ta kasar ta yi barazanar shiga yajin aiki, da kuma yin zaman dirshan a rassan babban bankin kasar, matukar bai dauki mataki nan da Litinin din makon gobe ba.
Source:
Rfi
Via:
Katsina City News