Taron na Yini daya ya karkata ne akan nuna muhimmancin karbar Allurar Rigakafin Korona.
Taron wanda kungiyar Mata ‘Yan jarida ta kasa reshen jihar Katsina ta shirya hadin gwiwa da hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOWA da kuma Asusun Tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, mai Ofishi a Kano, kuma an gudanar da shi a Katsina. Majiyar mu ta Radio Najeriya ta kawo cewa: “Taron karawa juna sani da aka shiryawa ‘yan Jarida dake aiki a gidajen yaa Labarai da kungiyoyin sa kai na fararen hula suka halartar, manufar taron yanada nufin wayar da kan mahalarta taron ta yanda zasu fadakar da al’umma akan muhimmancin karÉ“ar Allurar Rigakafin Korona. A jawabi maraba wakilin hukumar gyaran akida ta kasa NOWA a wajen taron Malam Husaini Sale yace taron yazo a kan lokaci idan akayi la’akari da muhimmancin wayar da kan jama’a akan amincewar Amsar Allurar Rigakafin cutar Korona.” Yace saboda muhimmanci da tasirin da ‘yan jaridu suke dashi yasa mukayi hadin gwiwa dasu domin ganin cewa sun bada tasu gudumawa don shawo kan wannan matsala, yace taron yanada muhimmanci ga jama’a duba da irin mutanen da aka hada a Wajen. Itama wakiliyar ta UNICEF Sa’adiyya Badamasi tayi jawabi sosai a wajen taron, akan irin kokarin da hukumar ta UNICEF takeyi, sana ta nuna jin dadin ta ganin irin yanda mahalarta taron suka nuna kwarewa wajen wayar da kan jama’a akan mahimmancin amsar Allurar Rigakafin ta Korona. A nata jawabin shugabar kungiyar mata ‘Yanjarida ta jihar Katsina Hajiya Hannatu Muhammad tace taron nada nufin fadakar da mahalarta don suma su wayar da kan al’umma na muhimmanci amsar Rigakafin Korona.