Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsinq City News
Rahotannin da Katsina City News ta hada a Safiyar Litanin zuwa yammaci, ta Hanyar tattaunawa da kuma gani da ido game da halin da Bankuna suke ciki, masu cire kudi da masu maida tsaffin kudi, abin sai dai “Lahaula wala ƙuwata illa billahi” Inji wani da muka iske a bakin Banki.
Wakilinmu ya jiyo ra’ayoyin jama’a daban-daban akan wannan yanayi da suka shiga sakamakon Canjin kudi, inda da dama daga wadanda muka iske bakin bankin suna Allah wadarai da Gwamnatin da ta jefasu cikin wannan yanayi. “Idan da tun farko da aka saki sabbin kudi Bankuna basu ɓoye ba suka dunga bawa ‘Yan alfarma, da ba a shiga halin da aka shigaba yanzu, kuma ni ke fadimaka duk da wa’adin ya kusa karewa yanzu idan kashiga banki cire kudi tsaffi zasu baka.” Inji wani da muka tarar a Layi.
Wata matashiya ta sheda mana cewa tun karfe tara na safe take a bakin banki itace keda lamba ta 299 har ya zuwa karfe biyu na hada wannan rahoto amma bata samu shiga banki ba.
“Ni kaina nayi kokarin shiga bankin access don isar da wani sako amma da masu gadi da mutanen da ke jiran layi suka rufar mani akan ba zani shigaba”. Inji wakilinmu.
Ya zuwa yanzu dai saura kwana takwas wa’adin daina karbar tsaffin kudi da babban Bankin Najeriya CBN ya bayar ya cika, a yayin da ‘Yan Kasuwa mafiya yawa suka kayyade 25 ga watan Janairu zasu daina karbar tsaffin kudin.
Shin ko Bankin Najeriya CBN zai kara wa’adin daina amsar tsaffin kuɗin ko a’a? Tambayar da kowa ke yi kenan abin jira shine ranar 31 ga watan Janairu da abinda ka iya biyo baya.