
-Ra’ayoyin mutane a Bakori
Daga Awwal Jibril a garin Bakori
@Katsina City News
A ranar Alhamis 19/1/2023 ne, jama’ar garin Bakori da ke Jihar Katsina suka wayi gari da labarin tsige Makaman Katsina, Hakimin Bakori, Alh. Idris Sule Idris daga mukaminsa, bisa zargin da aka ce an bincika an tabbatar.
Kamar yadda wata takarda da aka raba wa manema labarai mai dauke da sa hannun Kauran Katsina Hakimin Rimi, ta bayyana, an masarautar Katsina ta tabbatar da zarge-zargen da ake yi wa tsigaggen Hakimin.
A kan haka ne muka je garin na Bakori domin jin ra’ayoyin al’umma kan matakin da gwamnatin Jihar Katsina, tare da masarutar ta Katsina suka dauka kan tsohon Hakimin na Bakori, Alh. Idris Sule Idris.
Alh. Ahmad Mai Gadaje Bakori ya ce; “Zahirin gaskiya da ma gwamnati ba ta furta cewa saboda sha’anin tsaro ne ta cire shi ba. Ya fi kawai su ce su ce sun cire shi sai su yi shiru da bakinsu. Domin gwamnati ta fi karfin kowa. In dai a kan ta’adanci suka cire shi, in za ka tara mutum 1,000 a garin nan za su musanta maka wannan ikirarin na gwamnati.
“In a maganar tsaro ne, to ana jinjina mana a nan Bakori. Kamata ya yi a ce siyasa ce ta sa ta tsige shi. To da wannan ba komai don mun san su ke da iko,” in ji shi.
Malam Sani Ahmad Mai Chaji, kuma jigo a sha’anin tsaro a garin na Bakori cewa ya yi; “Hakimin Bakori ba a yi masa adalci ba. Domin a Bakori ba wani mutum da zai yarda da zargin da ake masa, domin jigo ne a ba da kariya a garin da dukkanin gudunmuwa. Kuma mu saboda shi muka shiga hidimar sama da tsaro. Siyasa ce kawai ta sa aka tsige shi.”
Malam Haruna Bakori ya ce; “Wannan ai abin dariya ne, wai yaro ya tsinci hakori. Kawai dai wasan kwaikwayo ne. Mu abin da kawai ke ba ta mana rai shi ne, bata wa Sarkinmu suna da suka yi a idon duniya. Shi kadai ne babban bakin cikinmu da damuwarmu.
“Kuma wa ya taba gani, ko ji an hada kai da Mai Girma Makama Alh. Idris Sule Idris ta kowabce irin hanya. Ko a dauki mutum a ce an bi ta hannunsa an amso shi, ko wata mu’amala ta daban ko wacce iri ce?”
Shi ma wani jigo a jam’iyyar APC da ya nemi mu sakaya sunansa cewa ya yi; “A wannan matakin da gwamnati ta dauka kan Makama Alh Idris Sule Idris, ba karamin abin kunya ta ja mana ba. Domin gaskiyar magana a dai yi sha’ani, kuma iyayen gidanmu ba su yi tunani ba.”
A irin garuruwan da ke karkashin masarautar nan irin su Kabomo, Marabar Danja, Kurami, Layin Ajiya da Buzaye da sauran su, duk dimbin mutanen da muka ji ra’ayoyinsu sun yi tir da faruwar lamarin na tsige Hakimin Bakori da aka yi.
Sannan wasu majiyoyi masu yawa suna zargin Hom. Amiru Tukur, dan Majalisa mai wakiltar Bakori da Danja a Majalisar Dokoki ta Taraiya da hannu dumu-dumu wajen sa wa a tsige Hakimin na Bakori, saboda in ya fadi zabe a wannan karan sai gwamnati ta nada shi a matsayin Makaman Katsina, Hakimin Bakori don sarautar ta koma dakinsu kamar yadda take a baya.
Duk kokarin jin ta bakin Hon. Amiru Tukur Makama don jin ta bakinsa, ko wani na kusa da shi, abin ya ci tura.