Jim kadan bayan CBN ya sanar cewa za a yi canjin kudade, sai Ministar Kudi ta yi karin haske game da lamarin tare da cewa a watan January na sabuwar shekara 2023 za su gabatar da tsarin Cashless Policy.
A shekarar da ta gabata CBN ya haramta harkallar kudaden yanar gizo Cryptocurrencies, sannan ya gabatar da wani sabon tsarinsa na kudin yanar gizo mai suna eNaira don riko da cigaban zamani da maye gurbin Crypto da shi.
eNaira ba shi da bambanci da kudin da yake asusunka wanda kake cinikayya da shi a wayarka na bankinka na FirstBank ko Union Bank da makamantansu, don haka ba hanyarsu daya da kudin Crypto ba saboda hawa da saukan da Crypto yake yi.
To, yanzu CBN yana son gabatar da tsarin Cashless Policy wanda yake ganin cewa zai kawo babban cigaba da rage wahalhalu na harkallar manyan kudade, da fadada tattalin arziki, da toshe hanyar biyan miyagu da haramtattun hanyoyi.
Ga abubuwan da za su faru idan aka gabatar da wannan tsarin:
—Za a daina harkallar manyan kudade a hannu
—Za a daina biyan miyagu (kidnappers) da manyan kudade
—Duk abun da mutum zai yi da kudi ana ganinshi (CBN da EFCC)
—Duk wani yunkuri da za ka yi na kudi hukumomi sun san da shi
—Za a dakile harkallar haramtattun kudade da cin hanci da rashawa
—Daga ina kudi yake kuma ina zai je, duk gwamnati ta sani
—CBN zai rage buga kudade
Cashless Policy dai ba sabon tsari ba ne, an fara gabatar da shi tun watan January na shekarar 2012 don habbaka cigaban kasa. A yanzu kuma ana son tabbatar da kasantuwarsa a ko’ina a fadin Nigeria, kamar yadda gwamnan CBN Godwin Emefiele ya fada.
Hukumar NBISS ta ce an samu kari sosai a kan kudaden da ake cinikayya da su ta wayoyin hannu (mobile device transaction) daga N719.4 billion a shekarar 2021 zuwa N1.8 trillion a wannan shekarar ta 2022.
Haka nan harkallar kudaden da ake yi a POS shi ma ya kai N663 billion a wannan shekarar. Inda yawan POS din da ke Nigeria ya kai 1.1 million (Statista)
Muhammad Auwal Ahmad (mohidden)