Ya ce Shugaban ya bata rawarsa da tsalle a karshen mulkinsa
Fitaccen marubucin nan na Najeriya, Farfesa Wole Soyinka, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bata rawarsa da tsalle saboda kirkiro sauya fasalin kudi yana dab da barin mulki.
Soyinka ya ce matakin ya goge dukkan alheran Shugaban kuma zai bar mulki a daidai lokacin da ’yan kasar ke fushi da shi.
Ya ce, “Ni a ganina, bai ma kamata mu bata wani lokacinmu mai amfani ba wajen auna gwamnatin Buhari, saboda zai tafi kowa na jin haushinsa.
“Ina magana ne a kan abin da dare daya ya jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin halin ni-’ya-su. Ina fargabar da za a fita jin ta bakin jama’a, to da za a fahimci cewa wannan matakin guda daya ya goge dukkan alheran gwamnatinsa.” in ji Soyinka.
Kazalika, marubucin ya gargadin ’yan Najeriya a kan yada labaran karya, inda ya karyata wani labari da ake yadawa a kansa a kafafen sada zumunta na zamani.
Ya kuma yi alkawarin bayar da tukwicin Dalar Amurka 1,000 ga duk wanda ya taimaka wajen zakulo wadanda suka kirkiri labarin tun da farko, wanda ake alakantawa da shi.