Fadar shugabancin kasar Najeriya, ta ce babu wata jihar da aka ba wa izinin siyan makamai masu sarrafa kansu ga jami’an tsaron da ba na gwamnatin tarayya ba.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Ya ce shugaban kasar ya sha bayyana wa karara cewa babu wanda aka yarda ya dauki AK-47 ko wani makami mai sarrafa kansa ba bisa ka’ida ba kuma dole ne ya mika shi ga hukumomin da abun ya shafa.
Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo a ranar 22 ga watan Satumba ya soki gwamnatin tarayya kan cewa tana adawa da shirin amfani da makamai da ake son bawa jami’an sa kai na Amotekun, bayan da ta kyale amfani da makamai a jihar Katsina.
Gwamnan ya bayyana kudurin sa na samar wa Amotekun makamai, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.
Ya ce matakin, tamkar tauye hakkin Amotekun ne na rike makamai domin kare al’ummar jihar.