Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa ‘yan banga a dajin Yargoje cikin ƙaramar hukumar Jibia a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar ya ce harin wanda ‘yan bindiga suka kai ya yi sanadin mutuwar ‘yan bangar da dama.
‘Yan bindigar sun yi wa ‘yan bangar kwanton ɓauta a dajin a lokacin da suke ƙoƙarin ƙwato wasu shanu da aka sace.
Shugaban ƙasar ya bayyana alhininsa kan rasuwar ‘yan bangar tare da jajanta wa iyalansu, yana mai cewa Najeriya ba za ta manta da sadaukarwar da suka yi na kare ƙasa, tare da yaƙar miyagun laifuka a ƙasarsu ba.
“Muna addu’a tare da jajanta wa iyalan mamatan a wannan lokaci na alhini. Muna addu’ar Allah ya gafarta musu” in ji Buhari.
Jihar Katsina da sauran jihohin arewa maso yammacin ƙasar na fama da matsalolin ayyukan ‘yan bindiga, waɗanda ke yawan kai hare-hare, tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.