Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin kamo ƴan bindigan da a ka rawnaito cewa sun karbe jami’an hukumar tsaron farar hula, NSCDC.
Buhari ya kuma bayyana “ɓacin ransa” game da kisan jami’an tsaron na Civil Defense guda bakwai da ‘yan fashin daji suka yi a Jihar Kaduna, yana mai ba da umarnin a kamo su.
BBC ta rawaito cewa wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa ta ce shugaban wanda ya siffanta kisan da “tsautsayi”, ya jinjina musu “saboda sadaukar da rayuwarsu ga ƙasa Najeriya”.
“Ina jimami tare da ‘yan uwan waɗanda aka kashe da kuma abokan aikinsu. Allah ya ba su da kuma hukumar haƙurin rashinsu,” in ji Buhari.
Sanarwar da Garba Shehu ya fitar a yau Alhamis ta ƙara da cewa shugaban ƙasa ya umarci sojojin Najeriya su bi sawun ‘yan fashin da suka kashe su “don bi musu haƙƙinsu”.