Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da matakin hukumar zaɓen ƙasar na dakatar da kwamishinanta na jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari, ya zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Tuni dai hukumar zaɓe ta damƙa batun Hudu Ari hannun babban sufeton ‘yan sanda don ya binciki halayyar kwamishinan a lokacin zaɓen cike giɓi na jihar Adamawa.
Shugaba Buhari ya umarci gudanar da bincike da gurfanar da Hudu Ari gaban shari’a, matuƙar an same shi da hannu.
Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na Sakataren Gwamnatin Tarayya Willie Bassey ya fitar, ta kuma ambato Buhari yana umartar babban sufeton ‘yan sanda da babban daraktan hukumar tsaron farin kaya DSS da babban kwamandan hukumar tsaro ta Civil Defence, su ma su gudanar da bincike kan rawar da jami’ansu suka taka wajen taimaka wa Barista Hudu Yunusa Ari.
Ya kuma buƙaci ɗaukar matakin ladabtarwa kan duk wanda aka samu da laifi.