Gwamnatin Najeriya ta amince da kashe naira miliyan N580.5 don sayo motoci masu silke da zimmar yaƙi da miyagun ƙwayoyi da hukumar National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA).ke yi.
NDLEA na ƙarƙashin kulawar ofishin Ma’aikatar Shari’a wadda kuma ita ce ta gabatar da ƙudirin neman sayen motocin, kamar yadda Ministan Shari’a Abubakar Malami ya faɗa wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa na yau Laraba.
A cewarsa: “Daliln da ya sa aka gabatar da ƙudirin shi ne don a nemi amincewar majalisar wajen bayar da kwangilar sayo motoci huɗu masu silke da ke da kujeru 14 ga NDLEA.”
Ya ƙara da cewa an yanke shawarar sayo motocin ne da zimmar kare rayuwar jami’an hukumar ta NDLEA “da ke aiki tuƙuru don ba da sakamako mai kyau”.
Kuɗin sun ƙunshi kashi 7.5 cikin 100 na kuɗin harajin VAT na tsawon mako 16, a cewar ministan.