Karim Benzema ya lashe kyautar zakaran ƙwallon kafa na shekara mai suna Ballon d’Or a karo na farko a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.
Kyautar dai ta zamto lada ne ga gagarumin ƙwazon da Benzema ya yi a kakar wasa ta 2021-2022.
An dai bada kyautar ne a wani biki da ya gudana a wani dakin taro na Theatre du Chatelet da ke Paris.
Kyaftin din Real Madrid Benzema, ya kasance wanda aka fi sa ran zai lashe kyautar a jiya Litinin bayan da ya ja ragamar da kungiyar ta Spain zuwa nasarar lashe gasar cin kofin La Liga da na Champions League a bara.
Gabanin gasar cin kofin duniya ta FIFA a watan Nuwamba zuwa Disamba, an canja tsarin cancantar lashe kyautar Ballon d’Or bisa ga kwazo a wasanni na yau da kullun a kaka a karon farko.
A maimakon a da sai a kan ƙwazon da ɗan wasa ya yi idan an shiga wata kakar wasannin.
Sai dai kuma dan wasan Faransa Benzema ya kasance kan gaba a kowane hali.
Sai gashi shi ne ya lashe gasar bayan ya zura kwallaye 44 a wasanni 46 kuma ya samu kambu na biyar a Turai a kakar 2021-2022.