• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Bello Turji ya tsira daga wani harin Sojojin saman Najeriya bayan kashe da dama daga yaransa.

admin-admin by admin-admin
September 18, 2022
in Sashen Hausa
0
Arangama tsakanin ‘Yan ta’addan Boko Haram da ISWAP
0
SHARES
64
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Akalla ‘yan Bindiga 12 ne, daga yaran​​fitaccen ɗan ta’adda, Bello Turji, aka kashe a wani samame da Sojoji suka kai ta sama.

An kashe su ne a wani samame da sojojin saman Najeriya suka kai a maboyar Turji a Kauyen Fakai da ke yankin Shinkafi a jihar Zamfara da yammacin ranar Asabar.

Mazauna yankin sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa, ‘yan ta’addan da ke halartar Bikin raɗin suna a gidan Turji, sun gamu da harin bama-bamai da aka yi musu ta sama.

Wata majiyar rundunar sojin saman da ke Katsina Makwabciyar jihar Zamfara wadda ta bukaci a sakaya sunanta saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai, ita ma ta tabbatar da faruwar lamarin.

Babban jami’in ya ce har yanzu ba a san inda Ɗanta’adda Turji yake ba izuwa safiyar Lahadi.

Wani tsohon kansila a yankin Fakai, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya ce ‘yan ta’addan na cikin wani masallaci da ba a kammala ba a lokacin da sojoji suka kai harin.

“Na bar garin don zuwa wajen sana’a ta a  Shinkafi da misalin karfe 1:58 na rana, ban kaiga isa inda nake ba a lokacin da na fara samun kiraye-kirayen cewa ana kai wa al’umma hari. Iyalina sun dauka ‘yan fashi ne suka kai hari amma sai suka yi waya suka ce sojojin sama ne. Ina jin rurin jiragen,” dan siyasar ya shaida wa PREMIUM TIMES a wata hira ta wayar tarho.

Ya ce wadanda aka kashe ‘yan bindiga ne (Maza da Mata) da ke cikin masallacin.

Idan shi (Bello Turji) yana cikin garin, kowa ya sani domin za ka ga mayakansa dauke da manyan makamai suna kare gidansa. An gudanar da sunan ne da safe yayin da ba a fara taron mata na yau da kullun ba da yamma,” inji shi.

Wani mazaunin garin wanda kuma ya nemi a sakaya sunansa ya ce ya kwashe iyalansa zuwa hedikwatar karamar hukumar Shinkafi.

“Na ga ’yan bindigar sun gudu a lokacin da muke kokarin buya. Kowa ya rude amma alhamdulillahi da jiragen ba su dade ba, da hakan ya shafi wasu daga cikin mu mazauna yankunan da ba su ji ba ba su gani ba,” inji shi.

Ya kara da cewa har ya zuwa daren ranar Asabar, ba a sami rahoton jikkata fararen hula ba yana mai jaddada cewa “mutanen sa (Bello Turji) ne kawai aka kashe.”

Majiyar ta ce kawo yanzu, an kashe mayakan Bello Turji 12 da wasu mata a harin.

Mai magana da yawun rundunar sojin sama ta Operation Base dake Katsina, Abdul Olaitan, bai amsa kiran waya da sakon kartakwana, da aka aika masa game da harin ba amma wani babban jami’i ya tabbatar da kai harin.

“Ba sansaninsa Bello Turji kadai ba. Mun fara kai hare-hare tun ranar Larabar da ta gabata,” in ji jami’in sojin saman.

Jami’in ya ce rundunar ta sama “sun sanya ido kan al’ummar tun ranar Juma’a. Kuma da muka samu cikakkun bayanai, muka shiga amma abin takaici, ba a kama shi a cikin gine-ginen da muka kai hari ba.”

Ya ce jami’an ‘Operation Forest Sanity’ ne suka kai farmakin da ‘yan ta’addan ‘Operation Hadarin Daji’ ta hanyar amfani da Mi 17 da Alpha jet yayin da wani jirgin kuma ya sa ido a lokacin harin.

Da aka tambaye su ta yaya suka san Bello Turji ba ya cikin wadanda aka kashe, sai jami’in ya ce “Muna da hotunan wuraren da aka kai harin kuma mun san wadanda abin ya shafa.”

Bello Turji ya yi kaurin suna wajen jagorantar kungiyar ta’addancin sa domin kai hare-hare a kan al’ummomi, tare da kashe mutane da dama da yin garkuwa da wasu.

Sai dai a watan Agusta gwamnatin Zamfara ta yi ikirarin cewa tayi Sulhu da shi.

Share

Related

Source: Premium Times
Via: Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Previous Post

Nigerian Air Force kills many terrorists but notorious leader Bello Turji escapes

Next Post

Rundunar sojin sama ta sake kai wa Turji farmaki

Next Post
Rundunar sojin sama ta sake kai wa Turji farmaki

Rundunar sojin sama ta sake kai wa Turji farmaki

Recent Posts

  • Dr. Dikko sworn in as Governor, takes over from Masari in Katsina State.
  • Tinubu Ya Nada Dele Alake A Matsayin Mai Magana Da Yawunsa
  • In inaugural address, Tinubu preaches unity, commitment to nation-building
  • Jawabin Farko a Matsayin Shugaban ƙasa: Tinubu ya cire Tallafin Mai gaba ɗaya
  • Malam Dikko Umar Radda ya zama sabon gwamnan jihar Katsina

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • May 2023
  • April 2023
  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.