• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Friday, March 31, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Bello Turji Ya Soma Kaddamar Da Hari Akan ‘Yan Bindigan Zamfara, Bayan Gwamna Matawalle Ya Masa Afuwa

August 21, 2022
in Sashen Hausa
0
Bello Turji Ya Soma Kaddamar Da Hari Akan ‘Yan Bindigan Zamfara, Bayan Gwamna Matawalle Ya Masa Afuwa
0
SHARES
83
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

…Bello Turji ya kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.

Daga Comr Abba Sani Pantami

Bello Turji, wanda Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya yi wa afuwa, a yanzu haka yana kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana hakan a yayin wani taro kan harkokin tsaro da kungiyar dalibai da wata jami’ar Madina ta shirya a Gusau babban birnin jihar.

Hassan ya yabawa Turji bisa matakin da ya dauka na ajiye ayyukan fashi da makami, da kuma matakin taimakawa wajen samar da zaman lafiya a kananan hukumomi uku da ke kan gaba wajen fuskantar hare-hare ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

A cewar mataimakin gwamnan, tun makwanni biyar da suka gabata ba a samu wata arangama tsakanin Fulani da Hausawa a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi na jihar ba, sakamakon tattaunawar sulhun da aka yi tsakanin bangarorin biyu da ke rikici da juna a jihar.

Gidan talibijin na Channels ya ruwaito mataimakin gwamnan na cewa, kwamitin da Gwamna Bello Matawalle ya jagoranta ya gudanar da taron zaman lafiya da sansanonin ‘yan bindiga tara a gundumar Magami da Masarautar Dansadau na kananan hukumomin Gusau da Maru na jihar domin su daina kai hare-hare ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ci gaba da cewa, Turji wanda Gwamna Bello Matawalle ya yi wa afuwa, a yanzu haka yana kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.

Share

Related

Source: Rfi
Via: Zaharadeen Mziag
Previous Post

International Art and Culture Craft: Katsina won best product design

Next Post

Dantakarar Gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP Engr. Nura Khalil ya Ziyarci jigon APC a Katsina Dakta Mustapha Inuwa

Next Post
Dantakarar Gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP Engr. Nura Khalil ya Ziyarci jigon APC a Katsina Dakta Mustapha Inuwa

Dantakarar Gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin Jam'iyyar NNPP Engr. Nura Khalil ya Ziyarci jigon APC a Katsina Dakta Mustapha Inuwa

Recent Posts

  • On birthday, clerics pray for Tinubu, Nigeria in Abuja
  • Gwamna Masari ya Kaddamar da Kwamitin Miƙa Mulki ga sabuwar Gwamnati
  • Masari: Tinubu Na Bukatar Addu’a
  • Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Karu Zuwa N46.25tr —DMO
  • FEC Approves N59.78bn For Ogoni Cleanup Projects

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In