Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasar Birtaniya (BBC) ta fara shirin rufe watsa shirye-shiryen Sashen Hausa. BBCn na yin shirin haka ne a wani 6angare na kokarin sauya sheka gaba daya daga talabijin da rediyo zuwa tashoshi na zamani.
Ba wai BBC Hausa kadai zai yi tasiri ba, har ma da sauran gidajen rediyo da talabijin, da suka hada da gidan talabijin na Somali TV da tashoshin talabijin na Afrique, wadanda suka zama amintattun hanyoyin samun bayanai ga al’ummar Afirka.
Da take kare matakin, BBC ta bayyana cewa sauya shekar ya zama dole domin dacewa da bukatu da dabi’un masu sauraronta.
“Bukatun masu sauraro da halaye suna canzawa, kuma mun san cewa akwai yuwuwar ci gaban dijital a fadin nahiyar,” in ji mai magana da yawun BBC Semafor.
Wasu ma’aikatan BBC sun soki wannan ra’ayi suna masu cewa ba dukkan ‘yan Afirka ne ke samun saukin shiga intanet ba, kuma kamfanin bai sanya kudin da ake kashewa wajen tsadar bayanai ba ga masu sauraron sa na Afirka miliyan 63.
Najeriya, Kenya, da Tanzaniya sun kasance uku daga cikin manyan masu sauraron kamfanin.
Canjin dijital na BBC zai haifar da babban hasara ga yawancin ‘yan jarida da ke aiki tare da kungiyar ta Afirka.