Janyewar ta biyo taron tattaunawa da akai da kungiyar ma’aikata da ministan Kwadago da ingantuwar Aiki, Dakta Chris Ngige a Abuja, ankafa wani kwamiti mai bangarori uku domin duba matsalolin ma’aikatan samarda wutar lantarkin Kamar yanda sanarwar tace.
Babban sakataren kungiyar kwadago Joh Ajiyoro ya bada tabbacin daukar matakan da suka kamata domin inganta samar da hasken wutar lantarki mai inganci a kasarnan.
Taron tattaunawar da ya dauki tsawon sa,o’i uku ya sanya ma’aikatan sunyi amannar cewa Gwamnati zata sauraresu kuma zata kula da inganta Ayyukan su.