Ahmed Badamasi
Tun Bayan daya ga watan October shekara 2022 wasu mambobi na kungiyar MAGPAMAN ake ta cire masu kudi a asusun ajiyarsu na bankin Eco Bank, wanda Kudin suke nuni da cewa ana cire su ne dan biyan bashi na kayan noman masara da aka basu bashi da ga babban bankin Nigeria ma’ana CBN.
Zonal Coordinator kuma tsohon Coordinator Mani L.G Abubakar Sulaiman Bujawa wanda ya samu wakilcin kungiyar MAGPAMAN yace “Wannan kungiya ce ta tallafin noman masara wanda a shekara biyu da ta gabata shuwagabanin mu na kasa suka muka basu jadawalin mutane wanda daga bisani mutane mutum 6605 sukayi nasarar samun wannan bashi, sai dai shugaban mu na kasa Prof. Edwin Uche ya rike kayan mutum 2004 Wanda ya sakar mana kayan mutum 4601.Naso ache State Coordinator da Secretary na jaha da kuma treasurer su cema shi Prof. Edwin Uche ina kayan mutum 2004, to wannan mutum 2004 duk kuna ciki kuma Shugaban mu na kasa ya rike ma mutum 2004 kaya.”
Bujawa ya cigaba da cewa “ga takarda daga national wadda tabada tabbacin za’a tsaidama kowa cire ciren kudin da ake masa.Wanda suke tataunawa da shuwagabanin jahohi da su basu list din wanda suka samu kaya, da wanda basu samu kaya ba kuma ana masu cire-cire duk zaa tsaida kuma abiya wanda aka Cire masu kaya basu.Bujawa yaba wanda aka cire ma kudi basu san hawa ba basu san sauka ba shawara da su kai kara kotu dan abi masu hakinsu kuma zai shiga gaba ya tabatarma kotu wlh baabasu kaya ba ba kuma ba abasu kudi ba abimasu hakinsu.
Shugaban kungiyar masu korafin MAGPAMAN wato MAGPAMAN Complainers Saifullahi Usman yace ” mu cike fam shekara biyu da ta gabata da zumar zaabamu bashin noman masara domin mu amfana da romon damokradiya, Sunana yayi nasarar pitowa cikin wanda suka samu wannan tallafi wanda daga bisani aka turoman #109,000:00 a account sabo da aka budemana na ECO bank naje incire kudi aka ce basu curuwa, shuwagabanin kungiya kawai ke iya pidda su haka na fara hada mutane muzo muyi yaki a Samu kudin nan inba haka ba wlh sai ancinye kudin asamu biyan bashi kuma lokacin babu kudin, anfara shirye-shirye a lokacin da tsare-tsare jama’a sai suka ja baya nakai har DSS office kuma nabasu takarda ina da copy amma mutane suka ki su goyaman baya dole na hakura na watsar nace nasan zaa zo irin wannan ranar.Yunzu gashi ana cirema mutane kudi ba gaira ba dalili akwai wanda aka cirema #392,000:00 akwai masu dubu dari biyu kudi daban daban nikuma gaskiya bansa kudi ba sai yasa har yanzu ba’a cireman ba.
Amma ba makawa tabbas sai mun sa wannan kungiyar kara kotu.
Sakataren kungiyar masu Korafin MAGPAMAN Malan Ibrahim yace ni maaikacin gwamnati ne kuma an cireman kudi amma zamu bi kadun abun har sai hakinmu ya fito.