Kwamishinan Kananan hukumomi da Masarautu na jihar Katsina Rt. Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo ya musanta wata takarda dake yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna cewa an cire zunzurutun kudi har kusan naira miliyan ɗari biyar don tarbar shugaban ƙasa da zaizo ziyara ta musamman a tsakanin 26 zuwa ashirin da bakwai ga wannan wata da muke ciki.
Gwajo-Gwajo ya bayyana cewa shi rabonsa da Ofis tun ranar Laraba, yana can wajen Kamfen Dantakarar Gwamna Dakta Dikko Umar Raɗɗa.
Kwamishinan yace a ranar Litinin kuma 23 ga wata an tashi da shirin gidan Radio na BBC Hausa wanda suka shirya muhawara a tsakanin ‘Yantakara kuma yaga yanada ra’ayi jin abinda Dantakararsu zai fada shine ya tafi can, bayan dawowarsa ya zarce gid don ganawa da Baƙi, yace don haka bai je Ofis ba, baisan da wata takarda ba.
Yace idan yaje Ofis yaga takarda zai duba yaga mi take cewa, koma wa ya turo, idan akwai bukatar a tsaya a duba koma waye za’a turawa sai a tura mashi.
Gwajo-Gwajo yace ita kardai idan har akwaita shi baisan abinda ta kunsa ba sai ya duba yaga mi za’ai mike cikinta. Ya bayyana cewa mai yiyuwa zarge-zarge ne kawai, yace sai a jira idan dagaske ne. Yaja hankalin al’uma akan su daina aiki da zargi.
A karshe ya tabbatarwa Al’ummar jihar Katsina cewa kudin ƙananan hukumomi naira Biliyan goma sunanan ba gara ba zago, sunma ƙaru bisa ga Bilyan goma.