Daga Muhammad Kabir
Jaridar Taskar Labarai
Dan Takaran Kujerar Gwamna a Jam’iyyar NNPP Engr Nura Khalil yace bannar da gwamnatin jahar katsina ta yi ma al’ummar jahar, gwara birai da su.
Dan takarar ya fadi hakan ne a lokacin da yake zan tawa da kwamitin tuntuba na yakin neman zaben Nura Khalil (Nura Khalil campaign organization contact and mobilisation committee).
Wadan da suka fito daga shiyoyin Funtuwa, Daura da shiyar Katsina. Taron ya gudana a dakin taro na Munaj event center Dake Cikin Birnin katsina ranar Lahadi 22/1/2023.
Nura Khalil ya Kara da cewa “Allah ya jarabemu, ya hada mu da shuwagabani, tsawon Shekara takwas Babu Wani Abu da sukai sai gallaza ma Mutane agaba.”
Dan takarar dai ya zargi gwamnati da sayar da kadarori waɗanda Shuwagabannin baya Suka Samar.
A taron Nura Khalil ya gabatar da manufofin sa da kudurorinsa guda goma (10) don samar da Sabuwar Jahar Katsina, yace zai samar da Tsaro, Noma da Kasuwanci, kawar da talauci, Ilimi, mayar da Yan gudun hijira, Bada cikakken Yanci ga ƙananan hukumomi, da dai sauransu.
Shima a nashi Jawabin Shugaban kwamitin Hon. Nasiru Umar Dutsinma ya bayyana cewa kowa ya sani lokuttan baya kamar wata biyu da suka wuce mai girma dan takarar gwamnan mu ya nada mu domin mu zagaya mu tattauna da masu ruwa da tsaki na wadannan kananan hukumomi da suka halarci wannan taro.
Daga karshe yayi kira ga mambobin da Suka halacci taron idan sun koma kananan hukumomin su subi mazabu mazabu da rumfunan zabe su fidda mutane biyar-biyar a karkashin su.