Babban bankin Najeriya ya samar da naira miliyan 120 domin badawa ga wakilanshi 750 suyi aikin canjin tsaffin kuɗaɗe a fadin jihar Katsina masamman ma a kananan hukumomin dake da ƙarancin bankuna.
Daraktan babban bankin mai kula da hadahadar kudade Ahmed Bello Umar ne ya sanar da hakan a lokacin taron manema labarai da ya gudana a reshen bankin na kasa dake Katsina.
Kamar yadda ya bayyana, wakilan su sun shiga kananan hukumomi Daura, Mashi, Mashi, kuma zasu shiga sauran kananan hukumomin jihar Katsina.
Ya kuma ce bankin na tura tawaga domin tabbatar da ganin bankuna na cika umarnin da aka basu; wanda suka haɗa da buɗewa a ranakun Asabar da Lahadi, sanya ma injinan ATM isassun kudade da kuma daina bada kudi cikin bankuna.
A kokarin ganin al’ummar jihar Katsina sun fahimci shirin, Ahmed Bello Umar ya ce sun saka hukumar wayar da kan yan Najeriya ta NOA.
Daraktan ya hakikance cewa, har yanzu babu wata sanarwar a hukumance dake ɗauke da labarin ƙara lokacin daina amsar tsaffin takardun kudaden.
Daga karshe babban bankin ya bada kafofin aike mashi da korafe korafe ta hanyar kiran wannan lambobin salular 08176657641, 08176657642 ko kuma aike mashi da sakon email ta adireshinshi mai suna “[email protected]”