@katsina city news
Yanzu haka Daya daga cikin manyan “yan ta addar yankin jibia Wanda ake Kira da suna Bala Wuta yana can cikin dajin kadobe, dake kudancin Mazanya, duk a karamar hukumar Jibia, yana Bukin aurar da “ya “yansa mata guda biyu.
Ganau sun ce “yan ta adda sama da dari uku sun hadu ana ta buki.
Ganau sun ce, Babura daga bangarorin zamfara da katsina sun cika dajin ana ta shewa.
Ganau, sun ce yanayin dajin da kuma inda suke,bukin motoci zayyi masu wahalar shiga koda kuwa na yaki ne.
Ganau sunce Jiragen yaki ne kadai ke iya kai dauki.ganau sunce ga alama “yan ta addar da niyyar buki suka zo bada niyyar fada ba.
Domin har zuwa dajin ba garin da suka kai ma Hari ko wawasa.suna wucewa ne salin alin
Hatta kauyukan da suka ke kusa da inda ake bukin ba su cema kowa komai ba.
@ www.katsinacitynews.com