An bayyana ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke a matsayin mutum ɗaya da ya fi sauran ‘yan takara samun karɓuwa ga jama’ar jihar Katsina.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin matashin ɗan siyasa injiniya Bashir Sani Dogo a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina.
Injiniya Bishir ya cigaba da cewa yadda al’umma ke tururuwar shiga jam’iyyar PDP kaɗai ya isa misali akan batun karɓuwar Sanata Yakubu Lado a wannan Iska mai kaɗawa.
“Taron ƙaddamar da yakin neman zaɓen sa da ya gudana a garin Funtua da kuma ƙaramar hukumar Ɓaure ya zama ishara ga jama’a musamman waɗanda ke wannan tafiya ba tare da an ba su kuɗi ba” inji shi
Ya ce, tunda yake siyasa bai taɓa ganin nasara da idansa ba, sai akan ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar PDP Yakubu Lado Ɗanmarke.
A cewar sa, Sanata Yakubu Lado ɗan kasuwa ne da yasan yadda ake maida naira goma naira dubu, ya ce zai yi amfani da wannan damar da yake da ita wajan bunƙasa tattalin arzikin da walwalar jama’a a jihar Katsina.
Haka kuma ya yi wa Katsinawa albishir da cewa biyan kudin makaranta (jarabawa) da ya gagara a wannan gwamnatin zai dawo kamar yadda aka san shi, ya ce Lado mutum ne mai kishin ilimin da kiwon lafiya da sauran bangarori more rayuwa.
Injiniya Bishir Sani Dogo ya ƙara da cewa Lado na sane da matsalar tsaro wanda ta hana al’umma da dama yin noma da kiwo, amma yana bada tabbacin cewa insha’Allahu Lado zai kawo gagarumin sauyi cikin ƙaƙanin lokacin idan an zaɓe shi.
“Idan ka kula da Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke baya juyawa akan abinda ya fi karfin sa, baya kula da masu yi masa hassada da yankan baya, abinda kawai yasa gaba shi ne, Allah ke bada mulki ga wanda ya so, a lokacin da ya so, kuma wajan sa Lado ke nema.
Injiniya Bishir Sani ya ƙara jinjinawa jama’ar da ke wannan hidima ta lado ba dare ba rana kuma da kuɗaɗen aljihun su suke amfani ba tare da an ba su ko sisi ba.
Daga ƙarshe ya yi ƙira ga jama’a da su tabbatar an zaɓi jam’iyyar PDP daga sama har ƙasa domin fitar da al’umma cikin mawuyacin halin da suke cikin sakamakon fadawa hannun waɗanda ba su iya mulki ba. (Yan sari)