Fatima Sa’ad @Katsina City News
Taron da ya gudana ranar Lahadi a filin taro na People square dake Daura da gidan Gwamnatin jihar Katsina, wanda ya shafi masu sana’ar hannu na kera kayan Daki,(Furnitures) da sauran su. wato Katsina Interior and Expo
Taron da Maigirma Gwamnan Katsina Rt. Hon. Aminu Masari yasamu halarta, da shugaban Kwamitin Katsina Interior Alh. Mustapha mai kudi Kankia, Mataimaka na musamman ga Gwamna Masari.A wurin taron an bayyana ma mai girma gwamnan jihar Katsina irin yadda kafintoci suke maida hankali wurin samar ma da yan jahar wasu nau’in kayayyaki dasuke sarrafawa, sannan kuma sun kuma nuna cewa zasu jajurce wurin yin wannan sana ‘ar ta Furnitures harma su Zarce kasashe da dama wurin aikin.
Sannan kuma shuwagabannin wannan taron sun bukaci gwamna daya samarma da kafintoci wani babbanwurin da zai zama nanne ainahin wurin da duk wani kafinta dake cikin jahar katsina zaya zauna domin gudanar da aikin su na kafin toci, yabada misalida idan aka ambaci kasuwar tsaye ansan wurine na sayar da waya, to suma suna son da asamar masu da wurin da zasu baje kolinsu na kafintocin jahar katsina.
Gwamnan na Katsina ya yaba matuka da jin dadi ganin cewa irin wadannan kayan ana kerasu a jihar Katsina inda ya kara masu Karfin gwiwa akan Yanda zasu maida hankali sosai domin suga cewa “Basai anje Dubai ba ko wasu kasashe don siyo furnitures”.