Rundunar ƴan sandan jihar Katsina a jiya Laraba ta dage cewa wasu ‘yan ta’adda da su ka kai hari karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina sun yi garkuwa da matasa 21 ne ba 39 kamar yadda wasu kafafen yada labarai su ka ruwaito ba.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa kakakin rundunar ƴan sanda a jihar, SP Gambo Isa, ya shaida mata cewa, matasan 21 na aiki ne a wata gona da ke kusa da kauyen Kompani Mayardua lokacin da ‘yan ta’addan su ka dira a wurin.
Isa ya ce jami’an tsaro na nan su na bin sawun ƴan ta’addan.
Wasu mazauna yankin sun ce ƴan ta’addan sun kewaye gonakin ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Lahadi, a daidai lokacin da matasan ke aikin girbin amfanin gona.
Matasan da suka hada da mata bakwai, maza 14 masu shekaru tsakanin 16 zuwa 21, an ce an dauke su aiki daga a da ke kewaye da gonar.
Wani mazaunin garin ya ce an sanar da shi a daren Lahadi cewa an sace ‘yar wansa tare da wasu da rana.
Ya ce: “Yar uwata tana shirin bikin aurenta. Ina tsammanin hakan ya sa ta tafi aikin gonar. An shaida min cewa ‘yan ta’addan sun nemi kudin fansa.”