…An karkatar da kudin katsina zuwa Kano
Muazu Hassan
@ katsina city news
A satin da ya gabata ne, ranar talata 7 ga watan febware gwamnan katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya gayyaci duk manajojin Bankuna dake jahar katsina da babban jami in CBN na katsina a wani taro gidan gwamnatin katsina akan matsalar ruwan kudi da ya shafi fadin kasar nan har da jahar katsina.
A taron gwamnan katsina, ya shaida masu damuwarsa akan yadda, al ummar katsina ke wahala a bankuna domin fitar da halaliyarsu da suka ajiye a bankunan.
Gwamnan ya shaida masu, cewa rahotonni daga jami an tsaro sun tabbatar masa da cewa, lamarin na iya chabewa idan ba a dau matakin gaggawa ba.
Manajojin Bankunan sun fada ma gwamnan katsina kai tsaye kuma ido da ido cewa sam babban Bankin kasa na CBN bai basu kudin da zasu saka a injin ATM na fitar da kudi ba.ko kuma su raba a bisa kanta.
Suka ce, suma sun damu da halin da ake ciki,suma mutane ne masu tausayi,amma ba yadda suka iya domin kuwa CBN ta hana su kudi.kuma ga babban jami in CBN zaune yana iya fada mana dalilin haka.suka kara jaddadawa
A taron Gwamnan ya tambayi Babban jami in na CBN yayi masu bayanin me ,ya Sanya katsina bata samu kudi ba?kamar sauran jihohin kasar nan ?
Babban jami “in yayi bayanin cewa,lallai CBN daga Abuja sun bayar da kudi a kawo katsina. Amma Wai jirgin yana isowa katsina ya tarar jirgin shugaban kasa,yana a filin jirgin don haka babu yadda za a yi,ya sauka don haka sai aka karkata akalar sa zuwa Kano.can ya sauke kudin katsina Mutanen kano suka amfana.
Gwamnan ya damu,ta kai a taron ya buga ma wani babban jami in CBN dake Abuja dan katsina.ya bayyana masa halin da katsina ke a ciki da yadda aka karkatar da kudin da za a kawo katsina zuwa Kano.
Babban jami in ya tabbatar ma da gwamnan katsina cewa za a samu kudi kafin satin ya kare.
A taron gwamnan ya soki yadda CBN ta tafiyar da aikin chanza sabon kudi ya kuma basu shawarwari.
Wata Majiya ta tabbatar mana da cewa.CBN sun kawo kudi a yammacin jumma ar data gabata.kuma ATM na bankuna zasu samu kudi a safiyar litinin 13 ga watan febware.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 email [email protected]