Kungiyar fafutuka da yaƙin neman zaben shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da Ɗan takarar Gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Umar Radda mai suna “Asiwaju/Gwagware Gida-gida Iniciative” Karkashin jagorancin Alh. Ibrahim Masari bisa kulawar Hon. Alh. Aliyu Ilu Barde ta shirya rabon kayayyakin Masarufi Irinsu Tufafi (Shaddodi), Tabarmi, Butocin Alwala da sauran su.
Da yake bayyana yanda tsarin raba kayayyakin yake, Hon. Aliyu Ilu Barde yace, rabon zai shafi Dukkanin ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina, wanda za’a raba Shadda Bandir Ɗari biyar, Butocin Alwala Dozin ɗari biyar, Barguna ɗari biyar. Dukkanin su ga Makarantun tsangayu, da gidajen Marayu da Talakawa marasa galihu.
Ya bayyana cewa za’a fara daga ƙaramar hukumar Katsina a ranar Lahadi inda aikin zaici gaba zuwa ko ina a faɗin jihar.
Kungiyar ta Asiwaju Gwagware Gida-gida Iniciative ta saba irin wannan rabon Tallafin ga marasa ƙarfi da masu lalura ta rashin lafiya, wanda ko a watannin da suka gabata kungiyar ta jagoranci kai tallafin kuɗi ga wata mata da Mijinta ya mutu ya barmata marayu mata, da kuma wani mai lalurar Kansar jini da kungiyar ta tallafawa da naira dubu ɗari biyu domin sayen magani.