Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Injiniya Dakta Muttaqa Rabe Darma mai bincike da Nazari akan wakokin gargajiya da Rayuwa Hausa, kuma Dan takarar Mataimakin Gwamnan Katsina a karkashin jam’iyyar NNPP. da yake gabatar da Kasida a ranar Hausa ta Duniya da ta gudana a ranar juma’a 26 ga watan Agustan da ya gabata garin Katsina yayi tsokaci akan hanyoyin da za’abi domin rayawa da tallata Al’adun hausawa a duniya.
Injiniya ya dauko mawakan hausa na zamani guda biyu gami da bada misalai akan wakokin su ta yanda suke shiga Sararin duniya a cikin dan kankanin lokaci, yace yakama ayi amfani da Basirarsu, da hazakarsu da mabiyan su (Masu sauraren su) domin tallata al’adun bahaushe ko da da shegantakarce.
Dakta Muttaqa Rabe ya bada misalin farko akan wakar Ado Gwanja daga garin Kano akan wakarsa ta WARR, Inda yace yayi nazarin ta daga lokacin da ya saketa a cikin wata daya, a shafin sa na YouTube, yace Mutum miliyan biyu da dubu dari daya sun kalleta a cikin wata daya, sana yace ita wakar a Duniya baki daya itace tazo ta Ashirin da hudu cikin wakokin da aka dunga kallo, yace a lura da kyau ita fa wannan wakar sabuwar waka ce, ba kamar sauran ba ta daya da tabiyu ko ta uku zuwa gaba, kila sunkai watanni ko shekaru da sanyawa. Dakta yace: kunga kadan daga tasirin wadannan mawakan, don haka yanada muhimmanci a hada gwiwa da su.
Injiniya ya kara bada misali na biyu akan wakar ta Ado Gwanja mai suna CHAASS Yace tunda akayita a kwana biyar zuwa shida yana duba Shafin mawakin na YouTube yace ba’a saketa ba sai bayan kwanaki biyu daga wannan lokaci. Yace: a yau zaman da ake wadanda suka Kalli Wannan wakar a shafinsa na YouTube (a ranar ta 26 ga watan Agusta) mutum dubu dari biyu da sittin da hudu, wanda ya nuna cewa duk rana mutum dubu dari da talatin da biyu suna kallon wakar, kuma mafiya yawa daga cikinsu Hausawa ne, ko masu sha’awar yaren na Hausa da al’adun bahaushe, idan zaka kara kididdiga zakaga ko wace awa daya mutum dubu biyar na Kallon wakar, ko wane Sakan daya mutum casa’in na kallon wakar, wanda ba’a karatun Kur’ani haka a yanzu, injishi.
Dakta yace idan kuwa haka ne, mai zai hana ayi amfani da irin wadannan mutanen mu sanyasu su dunga tallar al’adun Hausawa,? Yacea yasan wakar ta CHAASS yana Maganar Asosa, Asosa kuma waka ce ta yara, tun suna kanana ansanta, don haka yace Asosa waka ce ta Hausawa da Ado Gwanja ya nunata a cikin Al’adun Hausa kila da mutane sunma gane mi asosa take nufi da Hausa.
Duk acikin Kasidar Dakta Muttaqa Rabe ya sake zaluko wata waka ta Naziru Sarkin waka da yace, a cikin shirin Film mai dogon Zango na Labarina, yace shi tunda yake bai taba ganin waka mai mabiyanta ba wadda ta samu ‘yan Kallo a YouTube. Yace a cikin wata daya ankalli wakar mutum miliyan uku da dubu dari biyu. Yace idan da zaka raba miliyan uku da dubu dari biyu a kwana talatin, zaku ga a ko wace rana sau nawa aka kalleta.? A karshe yaja hankalin shehinnan hausa da suka taru a wajen cewa; suyi kokarin zaunawa da irin wadannan mutanen su hada gwiwa da irin matasan mawakan da ake saurare a yanzu, a gano hanyar da zasu rika tallata al’adun gargajiyar koda da shegantakar ne.