A 1951 Gwamnatin mulkin mallaka ta kafa gidan rediyon NBS a Legas tare da rassansa a Ibadan da Inugu da Kaduna. Tun a 1932 dai aka fara sauraron rediyo a Najeriya bisa tsarin RDS, amma baki dayan
shirye-shiryen na Ingilishi ne zalla. Don haka aka kafa NBS saboda a fara gudanar da shirye-shirye a Najeriya kuma cikin harsunan yan kasa. Wannan gidan rediyo na NBS shi ne ya fara saka karatun Alkurani Mai girma a tasharsa da ke Kaduna. Sai dai hakan ya jawo ce-ce- ku-ce. Domin kuwa Musulmi da ke Arewacin Najeriya sun koka da suka ji karatun Kurani a cikin naura ta ‘sharholiya irin rediyo wadda aka saba jin kade-kade da kuma zantuttukan duniya a cikinta. Don haka suka yi ta rubuta wasikun korafi zuwa ga
gidan rediyon inda suka bukaci a daina sa Kur’ani saboda yin hakan tamkar wulakanta shine. Sarkin Kano Muhammadu Sanusi shi ne Shugaban Hukumar Daraktocin Gidan Rediyon a wancan lokaci. Don haka a
wurinsa shugabannin gidan rediyon suka nemi mafita. A 1954 Sarki Sanusi ya dakatar da saka karatun Kurani a rediyo, inda ya nemi fatawa daga malaman Tijaniya na Kano da kuma Sarkin Zazzau Jaafaru dan Isiyaku, wanda shi ne wanda ake gani ya fi kowanne Sarki a Arewacin Najeriya ilimin addini a lokacin. Malaman Kano sai suka aike da fatawar zuwa ga Shehinsu Ibrahim Inyass. Amma sai baki ya rabu biyu. Shehi Inyass ya ba da fatawar cewa
saka karatun Kurani a rediyo ya halatta yayin da Sarkin Zazzau Jaafaru ya ce tunda yake babu wani nassi karara da ya bayyana halacci ko haramcin saka Kurani a rediyo, yana ganin gara kada a sa saboda kada a bude kofar keta alfarmar Littafi mai girma.
Ganin ansamu wannan sabani sai É—aliban Inyass na Kano suka tura masa da Fatawar sarkin Zazzau. Daga nan ya rubuto littafi mai taken “Alhujja al’baligha fi kaunil Iza’atul Æ™ur’ani Sa’igha. Inda anan ne yayi bayani cikakke tare da kawo gamsassun hujjoji cewa, sa karatun Ƙur’ani a rediyo ko bai kai matsayin wajibi ba, yakai matakin halal abin so.Â
Bayan samun wannan Fatawar ce aka ci gaba da saka karatun Alqur’ani a radiyo.