Daga Muhammad Kabir @Jaridar Taskar Labarai
Ɗalibai 40 ne suka anfana da kayayyakin sana’oi daban-daban da Shaidar kammala koyon sana’a daga Arewa Development Support Initiative (ADSI).
Anata jawabin, babbar bakuwa a wajen bikin Yaye Ɗaliban uwar gidan gwamnan jihar Katsina Hajiya Hadiza Aminu Bello Masari ta nuna jin dadinta abisa yadda kungiyar ta Arewa Development Support Initiative (ADSI) take koyar da samari da yan mata sana’oi daban-daban. Sana ta godena waɗanda suka kirkiro wannan kungiya.
Hajiya Hadiza Aminu Masari ta karfafa ma wannan kungiya gwiwa dasu cigaba da irin wannan aikin alkhairin domin al’umma su sami abin dogaru da kai.
Sana taja kunnen wadanda suka amfana da kayayyakin sana’o’in da suyi Anfani dashi ta hanyar da tadace.
Shima Shugaban Kungiyar ta Arewa Development Support Initiative (ADSI) Yace baya ga horas da matasa sana’oi Suna Wasu aikace aikacen na cigaban zama a, “Muna samun kuɗin shiga ga yayan kungiya.
Taron dai ya gudana a Muhallin dakin taro na Katsina Multipurpose Women Center dake Filin Samji a cikin birnin Katsina.