kungiyoyin sun yi arangamar ne tsakanin Dikwa da BamaImage caption: kungiyoyin sun yi arangamar ne tsakanin Dikwa da Bama
An yi wata arangama tsakanin kungiyar Boko Haram bangaren Abubakar Shekau da tsagen kungiyar karkashin ISWAP, a arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani babban kwamandan kungiyar mai suna Kundu.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne tsakanin Dikwa da Bama da ke jihar Borno.
Wata majiyar tsaro ta ce Kwamanda Kundu tare da tawagarsa na kan aikata fashi da makami, lokacin da mayakan ISWAP din a kan babura shida, kowanne dauke da mutum uku suka far musu.
A baya-bayan nan dai ana yawan samun arangama da juna tsakanin kungiyoyin da a baya suka addabi al’umar kasar,