Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya buƙaci hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana wa al’umar ƙasar adadin katunan zaɓen aka karɓa a faɗin ƙasar, gabanin babban zaɓen da ke tafe ranar Asabar.
Daraktan shirye-shirye da sanya idanu kan zaɓe na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar, kuma ministan ayyuka da gidaje na ƙasar Babatunde Raji Fasola ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gabatar ranar Talata a Abuja babban birnin ƙasar.
Ya ce ya kamata INEC ta bayyana adadin katin zaɓe da kowacce jiha da ƙaramar hukuma ta karɓa a ƙasar.
Ya ƙara da cewa “Mun shirya, mun bai wa wakilan jam’iyyarmu horo, mun kammala shirinmu game da zaɓen, dan haka muke ganin ya kamata INEC ta bayyana wa ‘yan ƙasa adadin mutanen da suka karɓi katin zaɓensu”.
“Ina ganin yin hakan zai taimaka wajen tabbatar da inganci da sahihancin zaɓen. An faɗa mana adadin mutanen da suka yi rajistar zaɓe, amma ba a faɗa mana yawan waɗanda suka karɓi katunansu ba, dan haka ya kamata mu tambaya”.
A ranar Asabar mai zuwa ne dai INEC za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun dokokin tarayya a faɗin ƙasar