Fassarar rahoton fact checks and statistics (FC&S)
@Katsina City News
Wata Cibiya da ake kira Fact Checks And Statistics da Turanci, wadda ta kware wajen fitar da sakamakon jin ra’ayin jama’a, ta yi bincike a kan ’yan takarar Gwamna a Jihohin Katsina, Kano, Sakkwato da kuma Kaduna a kan wacce jam’iyya za ta iya kai labari a zaben Gwamna mai zuwa?
Cibiyar, wadda ta saba fitar da irin wadannan sakamakon binciken akai-akai ta dau tsawon kwanaki tana aikinta a Katsina.
A Jihar Katsina sun yi aiki da wasu kungiyoyin masu zaman kansu na yanki da kananan hukumomin da suka yi bincikensu.
Cibiyar, wadda ba ta gwamnati ba ce, kuma ba ta aiki da kowacce Hukumar Gwamnati a wurin jin ra’ayin jama’a. Cibiyar ta dauki kananan hukumomi hudu a kowacce shiyyar Katsina guda uku, Daura, Katsina da Funtua, inda suka rika neman ra’ayin mutane kamar, matasa daga shekaru 18 zuwa 35, mata daga shekaru 18 zuwa 30, dalibai, sai kuma ’yan kasuwa, da mutane wadanda ba su da aikin yi.
Binciken Cibiyar ya gano cewa, kashi 70.1 na wadanda aka zanta da su sun fi gamsuwa da natsuwar da dan takarar jam’iyyar APC da na sauran jam’iyyun.
Kashi 69.3 na wadanda aka yi magana da su sun fi son a samu canji bayan wadannan shekarun 8 na APC zuwa jam’iyyar PDP.
Ra’ayin ya nuna cancanta da gogewar dan takarar NNPP, amma matsalar sabuwar jam’iyya da kuma rikicin cikin gida yana dushe karsashinsa.
Ra’ayin ya nuna cewa dan takarar da zai iya tasiri a nan gaba shi ne na jam’iyyar PRP wanda yana da kumaji da kuma bayyana komai a yadda yake. Rahoton ya nuna dan takarar dan siyasa ne mai amfani a Jihar Katsina nan gaba.
Ra’ayin dalibai da wadanda suka gama karatu ba sa aikin yi sun fi natsuwar cewa dan takarar APC zai fi duba lamarin su fiye da na jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyu.
Ra’ayin ya gano kashi 55 na masu fada a ji na jihar suna tsoron zaman dan takarar APC a matsayin Gwamna, suna ganin kamar ba zai zama Gwamna, ba wanda ya isa a bashi shawara ya dauka, yayin da suka dauki dan takarar PDP a matsayin wanda zai iya biya masu bukatunsu, amma shi ma zai yi abin da ya ga dama.
Rahoton ya nuna masu fada a ji sun nuna dukkanin manyan ’yan takarar guda biyu babu daya da za ka ba maki 55, amma duk wanda ya zama Gwamna ya samarwa kansa mukarrabai na gari shi ne zai yi nasara.
Rahoton ya nuna cewa, mutanen karkara ba su da wata matsaya a kan wane dan takara ne nasu, suna juyawa ne da juyawar bayanin da ya zo masu, sannan da kuma abin da aka ba su kafin ko ranar zaben.
Rahoton ya nuna shiyyar Funtua dalilai da yawa sun nuna a zaben jefa kuri’a jam’iyyar PDP tana gaba, sai APC na bi mata a baya.
A shiyyar Katsina, ana tafiya kunnen doki ne, amma cikin Katsina wadda ke da kuri’u masu yawa PDP tana gaba.
A shiyyar Daura, ana tafiya kunnen doki ne tsakanin jam’iyyar PDP da APC.
Rahoton kamar yadda jaridun Katsina City News ta ga kundin bayanan, babu wata jam’iyyar da ke da tabbas na cin zaben Gwamna da za a yi sai dai hasashe. Amma kowacce jam’iyya tana da wata madafa wadda ta dogara a kan ta ci zaben.
Idan jama’a suka fito da yawa suka kasa suka tsare, suka raka a duk fadin Jihar, wannan sakamakon sai bayan an sanar za a san yadda za ta kaya.
Idan amfani da mutane ne, APC ita ke da gwamnati, kuma ta tauna aya duk wata tsakuwa ta tsorata. Jami’anta masu rike da mukaman siyasa an gargade su kowa ya kawo inda yake.
Amfani da kayan masarufi da kudi a zabe wani abu ne, wanda har yanzu yana cikin abun da ba a kawar da shi ba. Gwamnatin APC ta shirya wa wannan.
Jihar Shugaban Kasa, tun da dimokaradiyya ta zo a kan kyale Jihar Shugaban Kasa ga jam’iyyar da Shugaban Kasa yake a ciki, ko wannan zaben ma haka za ta kasance?
A iya binciken rahoton, ’yan APC sun fi kumajin su halarci filin zabe fiye da ’yan PDP.
Rikicin PDP na cikin gida yana taba ta. Tsohon Gwamna Ibrahim Shema yana ta yakin sunkuru a kan jam’iyyarsa a Jihar. Wadannan dalilan da kuma wasu rahoton ya karkare jam’iyyar APC na iya sake kafa gwamnati a Katsina a zaben 2023, amma da kyar, kuma kuri’u dan kadan.
A zaben ’yan Majalisar Jiha, rahoton ya nuna za a yi majalisa ce wadda wata jam’iyya na iya rinjaye da hada kan wata jam’iyyar. Ko dai APC, ko kuma PDP, akwai yiyuwar NNPP za ta iya samu kujerun majalisar Jiha, haka ma PRP za ta iya samun kujera daya.
Katsina City News
@www.katsinacitynews.com
Facebook page/Group. Katsina city news.
You Tube Katsina City News TV
Twitter @Katsina City News
Jaridar Taskar Labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
@ www.thelinksnews.com