Photos 📸
A cigaba da Yakin neman zaɓen Dantakarar Gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Danmarke, a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina a ranar Talata 10 ga watan Janairu tawagar Dantakarar da magoya bayansa suka sauka Karamar hukumar Sandamu dake shiyyar Daura inda suka gabar da yakin neman Zaɓen 2023.
Magoya bayan jam’iyyar ta PDP daga Lungu da sako na ƙaramar Hukumar ne suka cika filin taron don shedawa da jaddada goyon bayansu ga jam’iyyar PDP daga sama har ƙasa.
Da yake gabatar da jawabinsa a wajen Shugaban Yakin neman Zaɓen kuma Sakataren Jam’iyyar PDP na ƙasa Sanata Ibrahim Tsauri ya jaddada sakon Dantakarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP Alh. Atiku Abubakar na cewa idan yazama shugaban kasa daga Ranar da aka rantsar da shi daga lokacin ya bude Bodojin Najeriya don Al’umma suji sauki.
A nasa jawabin Daraktan yakin neman Zaɓen na Atiku da Lado a jihar Katsina, Dakta Mustapha Moh’d Inuwa ya ja hankalin al’umma akan su gujewa mayaudara da zasu zo da kudi naira dari biyar ko fiye don su karbe ma (Musamman Mata Katin zaɓe) yace kada su yadda da wannan yaudarar. Ya bayyana cewa: Hukumar zabe tana bada katukan zabe a ko wane yanki, iya soyayyar da zaka nunawa Dantakarar shine kai maza ka amshi katin zabenka ranar ashirin da biyar ga wata ku Tandara APC da ƙasa. Injishi.
Sanata mai ci daga yankin Daura, Sanata Ahamad Babba Kaita ya bayyana irin alkawurran da jam’iyyar APC ta kasa cikawa yace idan har kuka saki kuka sake zaben jam’iyyar APC to babu abinda zata kawo maku sai rashin tsaro da wawushe kudaden kananan hukumomi, da kin biyan kudin makaranta ga yara da tsadar kayan masarufi.
Sanata Yakubu Lado Danmarke ya bayyana abubuwan da zai bawa muhimmanci irinsu Tsaro, Samar da takin Zamani mai Rahusa ga Manoma, don inganta Noma, Ilimi, Lafiya, Aikinyi da Bunkasa Sana’o,i.
A wajen taron Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina Alh. Magaji Ɗanɓaci ya karbi Jagororin APC aƙida da magoya bayansu su fiye da dubu ashirin da biyar 25 kamar yanda ya bayyana.