A ranar Lahadi 12 ga watan Maris Kungiyar Youths People Awareness Forum da Tallafin, Hon. Aliyu Ilu Barde jagoran Kungiyar Yaƙin neman Zaɓen Asiwaju Gwagware Gida-gida Initiative, ta kawo ƙarshen wasan da ta shirya domin ƙara danƙon Zumunci.
An gudanar da wasan ne, a Filin Fayis dake cikin birnin Katsina.
Wasan ƙarshen da akayi tsakanin ƙungiyar wasa ta Katsina City da kuma ƙungiyar wasa ta House Of Assembly, inda ƙungiyar Katsina City ta samu nasarar cinye Kofin da ƙwallaye 12.
Tin da farkon fara wasan Ƙwallon Fayis, Alhaji Aliyu Ilu Barde, shi ne wanda ya ɗauki nauyin gudanar da gasar kofin har aka kammala wasan ƙarshe.
Shugaban Ƙungiyar, Youths People Awareness Forum, Ahmad Abdullahi Katsina ya nuna jin daɗin sa ga al’ummar da suka jagoranci wasan tare da yin biyayya tin daga farkon fara gasar har zuwa ƙarshen ta.
Sakataren ƙungiyar, Sadiq Muazu Turaki, ya bayyana cewa, za su mara wa Dikko Radda baya duba da irin yadda ake yi ma su sha tara da arziki a kan gudanar da wasannin su, yace sun yi alƙawarin za su haɗa kai ga matasa ‘yan ƙwallo su yi ma shi ruwan ƙuru’u.
A lokacin da ake gudanar da wasan ƙarshe na gasar ƙwallon, Ɗantakarar Gwamnan jihar Katsina a inuwar jam’iyyar APC, Dr. Dikko Radda, Wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Ilimi na jihar Katsina, Farfesa Badamasi Lawal Charanchi, ya samu halartar wasan, tare da Protocol na Ɗantakarar Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, Alhaji Sa’idu Danja (Kogunan Jibiya), da kuma Kwamishinan Safiyo da Filaye, Bishir Gambo Saulawa, da Mannir Ibrahim Talba, da shugaban Kungiyar ta Asiwaju Gwagware Gida-gida Hon. Alhaji Aliyu Ilu Barde da sauran ‘Ya’yan Kungiyar ta Asiwaju Gwagware