Zaɓaɓɓen Ɗan majalissar tarayya mai wakiltar mazabar Katsina ta tsakiya Hon. Aminu Chindo, ya zargi gwamnatin jihar Katsina da yi mashi bita da kulli, domin ƙwace kujerar shi, bayan nasarar da ya samu na lashe zaɓen da gagarumin rinjaye.
“A wata zantawa da Hon. Aminu Chindo, yai da manema labarai, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina ta yi amfani da sakataren ilimi na ƙaramar Hukumar Katsina (ES) ya ɓoye takarardun makaranta ta domin a ƙalubalanci nasarar da ya samu a kotu.
An gudanar da zaben ne, a ranar Asabar 25 Ga watan Feb. 2023. inda Hukumar zabe ta ƙasa INEC ta bayyana Aminu Chindo a matsayin wanda ya lashe zaɓe da kuri’u 40,812 wanda ya doke abokin karawar shi na jam’iyyar APC Hon. Sani Ɗanlami da tazarar kuri’u sama da dubu goma sha baƙwai.
~ Katsina Reporters