@ katsina city news
An zabi Dakta Sameer Ismail Musawa cikin kwamitin yakin neman zaben Tinubu da Shettima kuma an saka shi bangaren hudda da wayar da kan jama a .
Zaben ya zo ne, a wata wasika da sakataren kwamitin na kasa Honourable James Abiodun faleke ya Sanya ma hannu a ranar 28/11/2022.
Wasikar ta ce, kwamitin yakin neman zaben ya rubuta cewa, an zabi sameer ne, saboda sanin da akayi masa na kishin kasa da neman kasar ta ci gaba, ya Sanya aka zabe shi.
Wasikar ta cigaba da cewa, Ana fatan zaiyi aiki tukuru don ganin nasarar APC a zabubbakan 2023
Wasikar ta cigaba da cewa,wannan aikin na kawo cigaba da kuma kishin kasa da jam iyya da dorewar Dimokaradiyya.
Sameer Dan kasuwa ne, Wanda kan shiga tsundum a duk harkokin Matasa da cigaban Al umma.
Ya sha samun lambobin yabo da kambin karramawa akan ayyukan shi.