
Daga Mohammad A. Isa Da Bin Yaqoub Katsina.
Bayan kwashe kimanin kwanaki 29 ana gudanar da tagwayen Tafsiran Al-ƙur’ani mai girma na watan Ramadan a Katsina wanda ’yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky (H) ke gabatarwa, daga karshe an rufe Tafsiran a ranar Talatar nan 27 ga Ramadhan, 1444H (18 ga Afrilu, 2023).
Tafsiran wadanda suka kasu biyu: na ‘yan’uwa Mata wanda Malam Muhammad Sani Lawal ke gabatarwa a duk Safiya a tsohuwar Markazin ‘yan’uwa da ke Unguwar Yari, sai kuma wanda Shehin Malamin, Shaikh Yakubu Yahaka ke gabatarwa ‘yan’uwa Burazu a Sabuwar Markaz da ke Kofar Marusa a kowane yammaci, an samu rufe tafsiran baki daya sai kuma in Allah ya kai mu badi; Tafsiran da Shaikh Yakubu Yahaya ya gabatar da jawaban rufewa.
A lokacin da shehin Malamin ke gabatar da jawaban ƙarshe a tagwayen muhallan biyu, Malamin ya fadakar tare da jan hankalin al’ummar Musulmi a kan halin da suke ciki na rarraba da kyamar juna, inda kusan jowa ya ja nashi 6angare ya ware.
Malamin ya kuma yi tsokaci a kan yadda wasu mutane masu da’awar masoya Annabi ne, amma suke ta6a janabin Manzon Allah ta hanayar je masa magannun raini, inda ya ce duk wanda raina Annabi daidai da silin gashin girar ido, ko yi wa Annabi to babu babu rahamar Allah, domin ya bar Musulunci.
“Wannan mummunar da’awar (ta raina Ma’aiki) an ƙirkire ta ne domin rusa addinin musulunci, da kafirta kowa madamar ba aƙidarsu yake bi ba”.
Har wayau Shehin Malamin ya yi kira ga al’ummar musulmi da su tashi tsaye don magance wannan matsalar tun kafin Allah ya yi fushi da wannan al’ummar baki daya, domin Allah da kansa yana girmama tare da tasasawa a yayin yi wa Annabi magana, to balle mu da aka yi don shi.
Abin da ke biye, wasu daga cikin Hotunan rufe tagwayen Tafsiran ne da mu ka ɗauko maku.