@ katsina city news
Rundunar yan sanda ta jahar katsina,tayi Nasarar kama Wanda ya jagoranci mummunan harin da aka kai a garin DanMusa, kwanakin baya.
Harin Wanda yayi sanadin mutuwar mahaifiyar Difi o da kuma “Dan ta da wasu mutane.
Lamarin da yayi sanadin kone kone da zanga zanga a garin na Dan musa
Wani tim na musamman a rundunar yan sandan katsina,shine ya samu nasarar kama duk wadanda sukayi wannan, ta ad
dancin.
Harin na, ta addacin a garin Dan musa,wani korarren Dan sanda ne, ya jogaranci kai shi.
Dan sandan, yana aikin shi, sai ya bace.ya bar zuwa aiki don haka, sai yan sanda suka dauka ya kori kansa da kanshi don haka suka dauke shi Wanda ya gudu ya bar aikin shi..
Mugun, ashe da ya bar aikin Dan sanda,sai ya koma wajen Barayin daji, yana masu safarar makamai yana kuma basu dubarun aikata ta addanci.
A ranar harin gidan mahaifiyar Difi o, ance kanen Difion ya gane shi har ya Kira sunan shi.
Wannan ya Sanya suka kashe shi,suka kuma kashe mahaifiyar don ana tsammanin taji lokacin da aka Kira sunan.
Wata Majiya tace, kama wannan korarren Dan sandan, yana ta tona asirin masu hada baki da wadannan miyagun, kuma suna ta shiga komar yan sanda.har yanzu yan sanda na kan binciken
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245