An gurfanar da tsohon mai shiga tsakani da ‘yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna Tukur mamu a gaban kotu, kan zarge-zarge 10 da suke da alaƙa da ɗaukar nauyin ta’addanci.
An dai kama Tukur Mamu ranar 6 ga watan Satumban 2022 a filin jirgin saman birnin Alqahira na ƙasar Masar a kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya, inda aka mayar da shi Najeriya.
Gwamantin Najeriya dai na zargin Tukur Mamu da taimaka wa ‘yan Boko Haram wajen shirya tare da ƙaddamar da hare-harensu kan ‘yan ƙasar da ba su ji ba, ba su gani ba..
Ana kuma zarginsa da karɓar maƙudan kuɗaɗe daga hannun iyalan fasinjojin jirgin ƙasan da ƙungiyar Boko Harama ta yi garkuwa da su.
An zarge shi karɓar dala 420,000 da kuma naira miliyan 21 daga hannun iyalan fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna.
An kuma zarge shi da ɓoye kuɗin da ake shirya ta’addanci a gidansa na jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar
To sai dai Tukur Mamu ya musanta duka zarge-zargen da aka karanto masa a gaban kotun.
Lauyan Tukur Mamu ya nemi da a bayar da belinsa saboda a cewarsa wanda yake karewar na fama da wani rashin lafiya da ke buƙatar tiyatar gaggawa.
To sai dai lauyan gwamnati ya nuna rashin amincewa da belin Mamu, yana mai cewa duk ciwon da ke damun wanda ake zargin ana iya magance shi a asibitin jami’an tsaron DSS inda yake tsare.
Haka kuma bayan doguwar muhawara alƙalin kotun mai shari’a Inyang Ekwo ya ce Tukur Mamu zai ci gaba da kasancewa a hannun jami’an DSS ɗin har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan bukatar belin nasa.