Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta ta fara karɓar sakamakon zaɓen gwamnan jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Kawo yanzu dai an karɓi sakamakon ƙananan hukumomi tarar – daga cikin ƙananna hukumomin jihar 21 -da ake gudanarwa a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke birnin Yola.
Manyan ‘yan takara biyu ne dai ke kan gaba a zaɓen jihar, waɗanda suka haɗar da gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP, wanda ke neman wa’adi na biyu, da kuma Sanata Aishatu Dahiru Ahmed Binani ta jam’iyar APC.
Ga yadda sakamakon ƙananna hukumomin da aka gabatar ya kasance:
Karamar hukumar Jada
ADC – 112
APC – 20899
PDP – 22933
SDP – 753
Karamar hukumar Gombi
ADC – 148
APC – 19665
PDP – 19866
SDP – 59
Karamar hukumar Guyuk
ADC – 55
APC – 14172
PDP – 18427
SDP – 422
Karamar hukumar Shelleng
ADC – 24
APC – 12589
PDP – 14867
SDP – 1136
Karamar hukumar Ganye
ADC – 80
APC – 21605
PDP – 17883
SDP – 69
Karamar hukumar Demsa
ADC – 255
APC – 11798
PDP – 22958
SDP – 146